28 Oktoba 2020 - 11:59
Buhari Ya Sake Nada Mahmood Yakubu A Matsayin Shugaban Hukumar Zaben Nijeriya (INEC)

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya sake nada Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC) a wa'adi na biyu bayan da ya aike da sunansa zuwa majalisar kasar don neman amincewarta.

ABNA24 : A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Buharin, Femi Adesina ya fitar ya ce shugaba Buharin ya tabbatar da sake nada Farfesa Yakubu ne a cikin wata wasika da ya aika wa shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmed Lawan.

Kafin hakan dai ana ta rade-radin cewa akwai yiyuwar a sauya shi daga wannan mukamin ganin yadda a makonnin baya shugaba Buharin ya nada wasu sabbin kwamishinonin zaben amma bai yi magana kan Farfesa din ba.

Yanzu dai ana jiran ita majalisar ce ta amince da bukatar shugaban kasar ko kuma akasin hakan.

A watan Nuwamban 2015 ne aka nada Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar (INEC) inda ya gaji tsohon shugaban hukumar Attahiru Jega wanda ya jagoranci zaben shekara ta 2015.

342/